Isa ga babban shafi
Najeriya-'Yan bindiga

'Yan bindiga sun kashe mutane 22 a Katsina, Zamfara

Akalla mutane 22 ne aka kashe, kana aka sace wasu 67 a hare hare dabam dabam da ake zargin ‘yan bindiga da kai wa a kauyukan jihohin Katsina, Zamfara da Kaduna a Najeriya.

'Yan bindiga sun addabi jihar Zamfara ta Najeriya
'Yan bindiga sun addabi jihar Zamfara ta Najeriya © dailypost
Talla

Wani jami’in hukumar agajin gaggawa ta jihar Katsina, Shamsu Yakubu ne ya bayyana haka jim kadan bayan da hukumar ta kai ziyara inda abin ya faru a Asabar, inda ya ce ‘yan bindigan sun  kashe 12, sukamkuma yi awon gaba da 38 a harin da suka kai garin Guga a karamar hukumar Bakori ta jihar.

Ya kuma yi bayanin cewa ‘yan ta’addan sun kona shaguna sama da 35, gidaje 11 da ababen hawa 6.

‘Yan bindigan sun kai hari garin Guga, Dukawa da Gidan Kanawa. Dukawa da Gidan Kanawa makwaftan juna ne a a karamar hukumar Funtua ta jihar Katsina.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.