Isa ga babban shafi
Najeriya

An gano gawarwakin mutane da dama da 'yan ta'adda suka kashe a Zamfara

Rahotanni daga jihar Zamfara da ke arewa maso yammacin Najeriya, sun ce an gano gawarwakin mutane fiye da 140, wadanda ‘yan bindiga suka kashe yayin munanan hare-haren da suka kai kan wasu kauyukan kananan hukumomin Bukuyyum da Anka a tsakanin ranakun Laraba da Alhamis.

Taswirar jihar Zamfara da ke arewa amso yammacin Najeriya.
Taswirar jihar Zamfara da ke arewa amso yammacin Najeriya. © Wikipedia
Talla

Wasu majiyoyi sun ce, daruruwan ‘yan ta’addan da suka kaddamar da munanan hare-haren, masu biyayya ne da kasurgumin dan fashin dajin nan Bello Turji, wadanda hare-haren jiragen yakin sojin Najeriya ya tilastawa tserewa daga sansanoninsu da ke dajin Fakai a karamar hukumar Shinkafi.

Wani mazaunin yankin da ya shaida aukuwar lamarin, ya shaidawa jaridar Daily Trust da ke Najeriya cewar, ‘yan ta’addan sun rika budewa mutane ciki har da mata da kananan yara wuta da miyagun bindigogi da zarar sun yi yunkurin tserewa daga gidajensu da maharan suka cinnawa wuta.

Zalika adadin kauyukan da ‘yan bindigar suka afkawa ya kai akalla 10, sabanin 6 da akasarin kafofin yada labarai suka ruwaito.

Sai dai har zuwa lokacin wannan wallafa babu karin bayani kan alkaluman wadanda wannan tashin hankali ya rutsa da su a hukumance.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.