Isa ga babban shafi
Najeriya - Zamfara

‘Yan Bindiga sun kai hari kan kauyuka 6 a Zamfara

‘Yan bindiga sun kai farmaki kan wasu kauyuka shida a jihar Zamfara, inda suka kashe mutane da dama wadanda ba a tantance adadinsu ba, lamarin da yayi sanadin raba daruruwan mutane. da muhallansu.

Wasu daga cikin makaman da yan bindiga suka mika zuwa hukuma a Zamfara
Wasu daga cikin makaman da yan bindiga suka mika zuwa hukuma a Zamfara REUTERS/Goran Tomasevic/File Photo
Talla

Kwamishinan yada labaran gwamnatin jihar Zamfara, Ibrahim Dosara ya tabbatar da kai munanan hare-haren yayin wata zantawa ta wayar tarho da kafar talabijin ta Channels a Najeriya.

Kwamishinan ya ce zuwa lokacin tattaunawar a ranar Alhamis basu kammala samun bayanai cikakku akan tashin hankalin ba.

Bayanai dai sun ce kauyukan da ‘yan ta’addan suka afkawa sun hada da, Lallaho, Kurfar Danya, Rafin Gero, Laho, Wanu, Barayar Zaki, da kuma Dutsin dan ajiya, wadanda ke kananan hukumomin Anka da Bukkuyum a jihar Zamfara.

Wasu mazauna yankunan da lamarin ya shafa sun bayyana cewar adadin ‘yan bindigar sun kai musu farmakin ya zarce 200 haye kan babura kuma dauke da muggan makamai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.