Isa ga babban shafi
Najeriya - Zamfara

Zamfara: 'Yan bindiga na barazanar kafa sabuwar daba a yankin Bakin Dutse

Al’ummar yankin tsafe ta yamma da ke jihar Zamfara sun bukaci taimakon gaggawa daga jami’an tsaro domin dakile yunkurin da gungun ‘yan bindiga ke yin a kafa wani sabon sansani a gaf da yankin nasu.

Hoton domin misali kan 'yan bindiga.
Hoton domin misali kan 'yan bindiga. © Depositphotos
Talla

Yayin karin bayani akan halin da suke ciki, wani mazaunin yankin ya shaidawa sashin Hausa na RFI cewa ko a baya bayan nan, sai da suka tsinkayi ‘yan bindigar akan Babura fiye da 10 da suka dunguma zuwa sabon sansanin da suke kafawa a kusa da kauyen Bakin Dutse.

A cewar majiyar tamu, tazarar sabuwar dabar  gungun ‘yan bindigar da kauyen na Bakin Dutse bai wuce nisan kilomita 3 ba, kuma sun mayar da wajen wurin ajiye mutanen da suka sace domin yin garkuwa da su.

Bayanai dai sun ce daga cikin gungun ‘yan bindigar akwai yara matasa da shekarunsu ke tsakanin 14 zuwa 17.

Dangane da ankarar da hukumomin tsaro kuwa, mazaunin yankin na Tsafe ta Yamma ya ce sun yi iyaka bakin kokarinsu wajen sanar da jami’an tsaro halin da ake ciki, amma har zuwa lokacin wannan wallafa suna cigaba da dakon samun taimakon da suka nema.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.