Isa ga babban shafi
Najeriya - Zamfara

‘Yan sanda sun cafke wata mata dauke da harsasai kusan dubu na AK47

Rundunar ‘yan sandan jihar Zamfara tare da hadin gwiwar takwarorinsu daga Abuja, sun cafke wata mata ‘yar shekara 30 mai suna Fatima Lawali dauke da harsasai 991 na bindiga kirar AK47.

Wata bindiga mai daukar alburusai 50.
Wata bindiga mai daukar alburusai 50. AFP - STEFAN HEUNIS
Talla

Kwamishinan ‘yan sandan jihar ta Zamfara, Mista Ayuba Elkanah, ya ce an kama matar ne a kusa da wata gada dake hanyar Sokoto zuwa Gusau, kafin ta shiga garin.

Matar da ta amsa laifin ta kuwa, ta ce ta dade ta na safarar makamai ga ‘yan bindiga a jihohin Sokoto, da Zamfara, da Katsina da Kebbi, da Kaduna da kuma Neja kafin ta fada hannun jami’an tsaro.

A cewar matar, ta yi bakin cikin kamata da aka yi, zalika tana neman gafarar iyalan wadanda suka rasa ‘yan uwansu a dalilin taimakawa ayyukan ‘yan bindigar da take yi, musamman mata irinta wadanda ‘yan bindigar suka kashewa mazaje da ‘ya’yansu, da harsasan da tayi safarar su ga ‘yan ta’addan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.