Isa ga babban shafi
Zamfara

‘Yan sanda sun musanta kashe jami’an tsaro 20 a Zamfara

Rundunar ‘yan sandan jihar Zamfara ta musanta rahotannin dake cewa ‘yan bindiga sun kashe jami’an tsaro kusan 20 akan hanyar da ta tashi daga Shinkafi zuwa Kauran Namoda.

Jami'an tsaron Najeriiya a harabar makarantar sakandaren Jangebe dake jihar Zamfara.
Jami'an tsaron Najeriiya a harabar makarantar sakandaren Jangebe dake jihar Zamfara. AP - Ibrahim Mansur
Talla

A wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar, Mohammed Shehu ya sanyawa hannu, rundunar ‘yan sandan ta tabbatar da harin amma ta ce jami’inta daya ne da kuma jami’an rundunar Civil Defence biyu ne suka rasa ransu a harin na kwanton Bauna.

Tun da farko dai rahotanni sun bayyana cewa wasu ‘yan bindiga sun yi wa jami’an tsaro wadanda akasari na hukumar tsaro ta Civil Defence da kuma ‘yan banga na yankin kwanton bauna karkashin jagorancin fitaccen jagoran ‘yan fashin daji mai suna Turji a ranar 28 ga watan nan na Oktoba.

Hoto domin misalin dake siffanta 'yan bindiga a Najeriya.
Hoto domin misalin dake siffanta 'yan bindiga a Najeriya. REUTERS/Goran Tomasevic/File Photo

Harin na Zamfara dai na daga cikin na baya bayan nan da ‘yan bindiga suka kai a yankin Arewa maso Yamma mai fama da matsalar rashin tsaro, inda ‘yan bindigar ke kisan mutane tare da garkuwa da wasu ciki har da yara ‘yan makaranta.

Ganin yadda matsalar taki ci taki cinyewa ne a baya bayan mutane da dama ciki har da gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufai, suka bukaci shugaban Najeriya Muhammadu Buhari da ya ayyana ‘yan bindigar a matsayin ‘yan ta’adda, matakin da tuni majalisar dokokin kasar ta nemi a aiwatar.

Sai dai a ranar Juma’ar da ta gabata, Ministan Tsaro, Bashir Magashi, ya ce Gwamnatin Tarayya na kan shirin tantance bin ka’idojin da ake bukata domin ayyana ’yan bindigar a matsayin ‘yan ta’adda.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.