Isa ga babban shafi
Zamfara-'Yan bindiga

'Yan bindiga sun aika wa al'ummar Shinkafi wasikar hari

‘Yan bindigar da ke shan ragargaza a hannun sojojin Najeriya sun aike da wata wasika ga al’ummar Shinkafi ta jihar Zamfara, inda suka sanar da shirinsu na kai musu farmaki.

'Yan bindiga sun addabi yankin arewa maso yammacin Najeriya.
'Yan bindiga sun addabi yankin arewa maso yammacin Najeriya. RFI
Talla

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da rahotanni ke cewa, ‘yan bindigar na dandana kudarsu a hannu sojojin Najeriya da aka tura su domin murkushe su.

Dr. Sulaiman Shu'aibu Shinkafi, daya daga cikin dattawan Shinkafi da a halin yanzu yake zaune a birnin Abuja, ya shaida wa RFI Hausa cewa, lallai wannan wasika ta tayar musu da hankali, yana mai kira ga gwamnatin da ta ceto garin Shinkafi daga wannan musibar.

Muna kira ga gwamnatin tarayya da ta yi kokari ta taimaka wa bayin Allah da ke cikin garin Shinkafi da kewaye domin wannan wasika ta tayar mana da hankali. Inji Dr. Shinkafi.

Kuna iya latsa alamar sautin da ke kasa domin sauraren bayanan Dr. Sulaiman Shu'aibu Shinkafi.

 

01:09

'Yan bindiga sun aika wa al'ummar Shinkafi wasikar hari

 

Dr. Shinkafi ya kuma bayyana cewa, sun samu rahotannin da ke tabbatar cewa, ana nan ana harbe-harbe a halin yanzu a garin.

Tuni dai gwamnati ta katse hanyoyin sadarwar wayar salula domin bai wa sojojin damar gudanar da ayyukansu na luguden wuta kan ‘yan bindigar yadda ya kamata.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.