Isa ga babban shafi
Najeriya - 'Yan bindiga

'Yan bindigar Zamfara na tserewa Katsina suna neman abinci da man fetur

A Najeriya, Mazauna karamar hukumar Kankara na jihar Katsina sun shiga rudani sakamakon kwararar 'yan bindiga da ake zargi masu tserewa ne daga Zamfara.

Yan bindiga a Najeriya
Yan bindiga a Najeriya © Daily Trust
Talla

Jaridar Daily Trust ta wallafa cewa 'yan bindigar na tserewa ne daga dazukan Zamfara inda ake musu luguden wuta zuwa kauyukan Katsina.

Wani mazaunin kauyen Pawwa, ya shaidawa jaridar cewa 'yan bindigar sun kafa shinge inda suke binciker mutanen da ke wucewa tsakanin titin Kankara zuwa Zango.

A cewar mutan yankin "Babban bukatar ‘yan bindigar yanzu shi ne samun abinci da man fetur, suna dauke da jarkoki, inda suke karbar wani adadi na mai daga masu ababen-hawa da kwace duk wani abinci da suka gani."

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.