Isa ga babban shafi
Najeriya-Zamfara

Ba za mu sake yi wa 'yan bindiga afuwa ba - Gwamnan Zamfara

Gwamnan Zamfara ta Najeriya Bello Matawalle, ya ce gwamnatinsa ba za ta sake yin afuwa ga 'yan bindiga a jihar ba domin kuwa bakin alkalami ya bushe a cewarsa.

Gwamnan jihar Zamfara ta Najeriya, Bello-Matawalle
Gwamnan jihar Zamfara ta Najeriya, Bello-Matawalle © Premiumtimes
Talla

Gwamnan wanda ya bayyana haka bayan halartar sallar Juma’ar nan da ta gabata a garin Gusasu, ya ce matakin soke yi wa ‘yan bindigar afuwa ya zama dole, saboda gaza rungumar shirin zaman lafiyar da gwamnati ta gabatar musu da farko.

Matawalle ya ce, a baya-bayan nan ‘yan bindigar suka aika masa da wani kwamiti mai karfi don rokon tsagaita wuta da kuma ba su damar samun kayayyakin abinci, amma ya yi watsi da bukatar, domin lokaci ya riga ya kure musu kan damar tuban da suka samu a baya.

Daga karshe gwamnan na Zamfara ya roki jama’a da su yi hakuri gami da goyon bayan sabbin matakan tsaron da gwamnati ta kafa don murkushe 'yan bindigar da suka addabe su.

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da 'yan bindiga suka shiga rudani, inda a yanzu suke karbar taliya da shinkafa a matsayin fansa saboda yunwar da ta addabe su biyo bayan daukar matakan hana sayar da man fetur da kuma hana su samun muhimman abubuwan more rayuwa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.