Isa ga babban shafi
Najeriya

'Yan bindiga sun sace Hakimi a Zamfara

Yan bindiga a Zamfara sun sake kai hari kan garin Adabka da ke karamar hukumar Bukkuyum.

Wani hoto domin misali dake nuna 'yan bindiga.
Wani hoto domin misali dake nuna 'yan bindiga. Getty Images/iStockphoto - zabelin
Talla

Bayanai sun ce maharan sun kai farmakin ne a ranar Asabar da misalin karfe 12 na rana har zuwa 4 na yamma inda suka yi awon gaba da Hakimi masarautar yankin na Adabka Alhaji Nafiu Shehu, sai dai babu babu wanda aka kashe a lokacin harin.

Zuwa lokacin wallafa wannan labari dai, rundunar 'yan sandan Zamfara ba ta tabbatar da kai harin ba, sai dai majiyarmu ta tabbatar da aukuwar lamarin da ya kai ga sace basaraken.

Adabka na da tazarar kilomita 165 daga Gusau babban birnin jihar Zamfara.

A wani labarin kuma, rahotanni sun ce mazauna garin Tsafe dake jihar ta Zamfara sun kasance cikin tsananin zulumi a karshen makon nan saboda barazanar hare-haren ‘yan bindiga.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.