Isa ga babban shafi
Najeriya - 'Yan bindiga

Sojin saman Najeriya sun kashe 'yan bindiga sama da 120 a dajin Zamfara

Akalla ’yan bindiga 120 ne suka mutu sakamakon hare-hare ta sama da jiragen yakin sojojin saman Najeriya suka yi kai musu a dajin Sububu da ke Jihar Zamfara.

Jirgin yakin Sojin Saman Najeriya da za a fara aikin farmakar 'yan bindiga da su.
Jirgin yakin Sojin Saman Najeriya da za a fara aikin farmakar 'yan bindiga da su. naij.com
Talla

Kafar yada labarai ta PRNigeria dake wallafa labaran da suka shafi tsaro a Najeriya ta rawaito cewa jami’an tsaron sunyi nasarar ce, bayan wasu bayanan sirri da suka samu daga yankin dangane da shige da ficen gungun ‘yan bindiga a dajin dake yankin Bububu.

Majayar tace, da farko sai da jiragen leken asarin  yakin suka gama nazartar dajin da kuma kai kawon ’yan bindigar kafin suka fara yi musu ruwan wuta ta sama.

“Bayan samun rahotannin sirri ranar 12 ga watan Yulin 2021 cewa wani gungun ’yan bindiga na hada ayari a dajin Sububu da Jajani da kuma Dammaka, an girke jirgin yaki domin ya yi nazari kafin kaddamar da harin”

 

Majiyar tace, an kasha kimanin ‘yan bindiga 125 yayin wannan hari, yayin da tsiraru daga cikinsu suka ranci na kare.

Jirgin sama mai saukar ungulu na rundunar sojin saman Najeriya
Jirgin sama mai saukar ungulu na rundunar sojin saman Najeriya BusinessDay

To sai dai Jaridar Daily Trust tace majiyoyin yankin sun tabbatar mata da cewa harin sojin saman yayi sanadiyar mutuwar wata Mata da ‘ya’yan ta hudu a Sububu.

Kakakin Rundunar Sojin Sama na Najeriya, Air Comondo Edward Gabkwet, ya tabbatarwa Jaridar PPNigeria harin, inda yace sun lalata baburan da ‘yan bindigar ke amfani wajen kai hare-hare da kashe bayin Allah, to sai dai baiyi Karin bayani dangane da kisan fararen hula ba.

Shugaban rundunar sojin saman Najeriya Air Marshal Isiaka Oladayo Amao
Shugaban rundunar sojin saman Najeriya Air Marshal Isiaka Oladayo Amao © NAF TWITTER

Yanzu haka Sojojin Najeriya karkashin rundunar Operation Hadarin Daji wacce ta kunshi sojoji da sauran jami’an tsaro ke yaki da ’yan bindiga a yankin Arewa maso Yammacin kasar domin kawo karshen su.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.