Isa ga babban shafi
Najeriya - Zamfara

'Yan bindiga sun kai hare-hare sasassan Maradun da Zurmi a Zamfara

Rahotanni daga jihar Zamfara a Najeriya sun ce ‘yan bindiga sun kashe mutane da dama yayin hare-haren da suka kai kan wasu yankunan kananan hukumomin Maradun da kuma Zurmi a ranar Asabar.

Wata bindiga mai daukar alburusai 50.
Wata bindiga mai daukar alburusai 50. AFP - STEFAN HEUNIS
Talla

A Maradun, bayanai sun ce maharan sun kashe manoma 8, tare da jikkata wasu da dama a kauyen Damaga, sai dai rundunar ‘yan sanda da tabbatar da kai harin ta ce bata tantance adadin mutanen da farmakin ya rutsa da su ba.

Wadanda suka tsira sun ce ‘yan bindigar da dama haye kan babura sun afkawa kauyen na Damaga ne a daidai lokacin da manoma ke aiki a gonakinsu da safiyar ranar Asabar.

A Zurmi kuwa majiyarmu ta ruwaito cewar akwai faragabar ‘yan bindiga sun kashe mutane kimanin 50 yayin hare-haren da suka kai wa garuruwan dake sassan karamar hukumar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.