Isa ga babban shafi
Zamfara

An kama sojan da ke bai wa 'yan bindiga makamai a Zamfara

Gwamnan Jihar Zamfara da ke Najeriya, Bello Mutawalle ya dakatar da dagacin Badarawa da ke masarautar Shinkafi, Surajo Namakkah saboda nadin sarautar gargajiya da ya yi wa wani soja da aka kama yana sayar da makamai ga ‘yan bindiga.

Gwamnan Jihar Zamfara , Bello Matawalle
Gwamnan Jihar Zamfara , Bello Matawalle © Premiumtimes
Talla

Mutawalle ya ce, gwamnatinsa ba za ta lamunci duk wani abu da ka iya lalata zaman lafiyar da jihar ta samu da kyar ba.

Babban Jami’in Yada Labaran gwamnatin jihar, Yusuf Idris ya sanar da dakatarwar ta sai baba ta gani  a yau Jumma’a.

An kama jami’in sojan ne a daidai lokacin da yake mika makamai ga wani mutum mai suna Kabiru Bashir na kauyen Maniya da ke Masarautar Shinkafi.

Rahotanni sun ce, sojan ya karbi  kafin alkalami na Naira dubu 100 daga hannun ‘yan bindigar.

Matawalle ya yi gargadin cewa, daga yanzu, dole ne sarakunan gargajiya su nemi amincewar gwamnati  gabanin nadin sarauta ga wani domin kauce wa jefa gwamnatin cikin abin kunya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.