Buhari ya bada umurnin murkushe masu garkuwa da mutane
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya yi Allah wadai da kashe-kashen ƴan bindiga dake kara ta’azzara a jihohin Zamfara da Kaduna.
Wallafawa ranar:
A cikin wata sanarwa da mataimakinsa kan harkokin yada labarai Malam Garba Shehu ya fitar, shugaban ya buƙaci sojojin ƙasar da su gaggauta kawo karshen matsalar a “yaren da yan bindigar za su fahimta.”
Wannan na zuwa ne bayan harin da ƴan bindiga suka kai a yankin Maradun a jihar Zamfara inda suka kashe sama da mutane 40.
Haka kuma ƴan bindiga sun kai jerin hare-hare a Kaduna inda suka sace ɗaliban makaranta a makon da ya gabata.
A cikin makon da ya gabata wasu mazauna yankin Sabon Tasha dake karamar hukumar Chikun a jihar Kaduna, sun gudanar zanga-zangar nuna bacin rai kan fargabar da ta mamaye su a dalilin fuskantar hare-haren ‘yan bindiga.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu