Isa ga babban shafi
Najeriya-Buhari

Buhari ya bukaci a kubutar da daliban Islamiyar da aka sace

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bukaci  hukumomin tsaro da na leken asirin kasar da su kara kaimi wajen maido da daliban makarantar Islamiya 200 da ‘yan bindiga suka sace a jihar Neja.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari © Nigeria Presidency
Talla

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da rahotanni ke cewa, ‘yan bindigar da suka sace daliban makarantar Jangebe ta jihar Zamfara, su suka yi awon gaba da daliban Neja.

Shugaba Buhari ya yi Allah-wadai da wannan al’amari , yayin da ya umarci hukumiomin tsaro na gwamnati da su agaza wa iyalan yaran da aka sace.

A ranar Lahadi ne ‘yan bindigar dauke da muggan makamai kuma haye a kan babura suka dirar wa makarantar  Islamiyar da ke garin Tegina na Neja , inda suka tattara dalibai da malamai suna tsaka da karatu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.