Isa ga babban shafi
Najeriya - Buhari

Shugaba Buhari na ziyarar aiki a birnin Maiduguri

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya sauka a birnin Maiduguri babbar birnin jihar Barno, dake zama mahaifar kungiyar Boko Haram.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari yayin da ya sauka a Abuja bayan ziyara a Faransa ranar 20 ga watan Mayun 2021.
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari yayin da ya sauka a Abuja bayan ziyara a Faransa ranar 20 ga watan Mayun 2021. © Femi Adesina
Talla

Da misalin karfe 9:30 na safiyar Alhamis shugaban ya sauka a filin jiragen saman birnin, inda mazauna garin sukayi ta wakokin girmamawa “Baba Oyo-oyo!”

Buhari na ziyarar aiki ne a jihar domin kaddamar da wasu ayyukan da gwamnatin Babagana Umaru Zulum ta aiwatar.

Shugaban kasar ya samu tarba daga gwamnan jihar Farfesa Babagana Zulum da mambobin majalissun dokoki na kasa dana jihohi da shuwagabannin hafsoshin tsaro da kuma manyan jami'an gwamnati.

Rangadi

Rahotannin na cewa shugaban zai ziyarci fadar mai martaba Shehun Borno, Kana zai yi jawabi ga sojojin da ke fagen daga a yaki da Boko Haram sannan ya kaddamar da wasu ayyuka da gwamnatin jihar da aiwatar a cikin babban birnin jihar.

Ana kuma saran shugaban zai wuce barikin sojin Maimalari domin ziyarar sojojin da suka ji rauni.

Tuni Shugaban ya kaddamar da ayyuka a Makarantar Sakandaren Fasaha ta Gwamnati dake Njimtilo, da Jami’ar Jihar Borno.

Tsaikon zirga-zirga

Masu ababen hawa dai sun fuskanci matsaloli kasancewar galibin hanyoyin cikin garin na Maiduguri a rufe suke, saboda ziyarar shugaban kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.