Isa ga babban shafi
Najeriya-Zamfara-'Yan bindiga

'Yan bindiga sun sace mutane 60 a Zamfara

Hukumomi sun ce ‘yan bindiga sun sace mutane 60  a wani sabon hari da suka kai wani kauye a jihar Zamfara dake Najeriya.

Hoton 'yan bindiga somin misali.
Hoton 'yan bindiga somin misali. © India TV News / PTI
Talla

A yammacin jiya Juma’a kwamishinan yada labaran jihar, Ibrahim Dosara ya ce ‘yan bindigar sun kutsa kauyen Rini dake karamar hukumar Bakura ta jihar a daren Alhamis, inda ya ce bayan sun tafi ne al’ummar kauyen nemi mutane 60 suka rasa.

A watan ganawa da ya yi da wata tashar talabijin a kasar, kwamishinan ya ce ‘yan bindiga sun zafafa ayyukansua a jihar ne sakamkon hare haren da sojin Najeriya ke kai musu ta sama da kasa.

Zamfara na daya daga cikin jihohin da ke fama da ayyukan ‘yan bindiga masu satar mutane don neman kudin fansa, inda daruruwan mutane ne aka sace ko aka kashe a cikin ‘yan shekarun nan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.