Isa ga babban shafi
Najeriya - Ta'addanci

'Yan majalisa sun bukaci Buhari ya ayyana ‘yan bindiga a matsayin ‘yan ta’adda

Majalisar dattawan Najeriya ta bukaci shugaban kasar Muhammadu Buhari da ayyana ‘yan bindiga masu garkuwa da mutane da kuma hare-hare cikin kasar a matsayin ‘yan ta’adda.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari.
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari. Twitter/@BashirAhmad
Talla

Kudurin da majalisar dattawan ta amince da shi, ya bukaci gwamnatin Buhari ta kaddamar da yaki a kan ‘yan bindigar, tare da fitar da sammacin kama shugabanninsu a duk inda suke.

A baya bayan nan ne dai cikin watan Satumban da ke shirin karewa gungun ‘yan bindiga masu yawan gaske suka  kai wani mummunan hari kan sansanin sojoji da ke Burkusuma a Karamar Hukumar Sabon Birni da ke jihar Sokoto ta Najeriya, inda ake fargabar sun halaka jami’an tsaro fiye da 10.

Rahotanni sun ce ‘yan bindigar sun kai harin ne da safiyar Juma’a a kauyen Dama da ke karamar hukumar ta Sabon Birnin.

‘Yan ta’addar sun kuma kai wani harin kan kauyen Katsira, inda nan kuma suka hallaka mutane hudu.

Wasu mayakan Boko Haram.
Wasu mayakan Boko Haram. AFP

A karshen watan Satumba, wasu majiyoyin sojin Najeriya suka shaidawa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa mayakan Boko Haram fiye da akalla 250 da suke biyayya da tsohon jagoransu Abubakar Shekau, sun fice daga sansaninsu da ke arewa maso gabashin kasar zuwa arewa maso yammaci, domin hada karfi da ‘yan bindiga a dajin Rijana da ke jihar Kaduna.

A cewar daya daga cikin majiyoyin gungun mayakan na Boko Haram ne suka kitsa wasu sace-sacen da ake yi a arewa maso yammacin Najeriya a baya bayan nan, yayin da kuma suke ci gaba da horas da ‘yan bindiga wajen sarrafa manyan bindigogin harbo jiragen sama, bama-bamai da sauran muggan makamai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.