Isa ga babban shafi
Najeriya - Buhari

Buhari na fuskantar tsananin matsin lamba saboda matsalolin tsaro

Yayin da Najeriya ke fama da tashe tashen hankula dake da nasaba da masu jihadi da na 'Yan bindiga da masu garkuwa da mutane, shugaban kasar Muhammadu Buhari na cigaba da fuskantar matsin lamba daga magoya bayan sa da ‘yan adawa saboda abinda suka kira gazawar sa wajen shawo kan matsalolin tsaro.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari da hafsoshin tsaron kasar a fadar gawamnatin Najeriya yayin ganawar gaggawa kan tsaro ranar 30 ga watan Afrelun 2021
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari da hafsoshin tsaron kasar a fadar gawamnatin Najeriya yayin ganawar gaggawa kan tsaro ranar 30 ga watan Afrelun 2021 © Presidency of Nigeria
Talla

Watan Afrilun da ya gabata shine mafi muni a Najeriya sakamakon zub da jini da kuma satar mutanen da aka gani, wanda ya nuna cewar a cikin mako guda kawai an kashe mutane akalla 240, yayin da aka sace sama da 50 kamar yadda kafofin yada labaran kasar suka ruwaito da suka hada da kashe daliban da aka sace da dakarun sojin da aka yiwa kwantar bauna da kuma Yan Sandan da barayin shanu suka hallaka.

An bukaci Buhari ya tashi tsaye kan tsaro

'Yan Majalisar Dattawa da na wakilai da ma fitaccen marubucin kasar Wole Soyinka sun bukaci shugaban Najeriya da ya tashi tsaye wajen dakile wadannan matsalolin tsaro.

Majalisar wakilan kasar ta bukaci shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya kafa dokar ta baci a fadin kasar, yayin da masu sukar sa ke cewa ya kasa daukar matakan da suka dace a wannan lokacin da ya dace.

Sanata Smart Adeyemi daga Jam‘iyyar shugaban ta APC ya bayyana cewar wannan shine rashin tsaron da Najeriya ta gani mafi muni, wanda yace yafi yakin basasa muni.

Alakar tsaro da zaben 2023

Wasu na danganta wadanan korafe korafen da ake samu kan tsaron da zaben shekarar 2023, amma ganin irin hare haren da ake samu ya sa 'Yan Najeriya da dama na tambayar ko tashe tashen hankulan sun fi karfin hukumomi ne.

Bayan wani taro majalisar tsaron da aka yi ranar juma’a wanda ya kunshi hafsoshin tsaron kasa, gwamnati ta sanar da cewar shugaban kasa Muhammadu Buhari ya shirya daukar kwararan matakai domin kawo karshen tashin hankalin da ake samu.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari da mataimakinsa da kuma shugabannin hafsoshin tsaron kasar a fadar gawamnatin Najeriya yayin ganawar gaggawa kan tsaro ranar 30 ga watan Afrelun 2021
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari da mataimakinsa da kuma shugabannin hafsoshin tsaron kasar a fadar gawamnatin Najeriya yayin ganawar gaggawa kan tsaro ranar 30 ga watan Afrelun 2021 © Presidency / Femi Adesina

Mai baiwa shugaban shawara kan harkokin tsaro Babagana Monguno yace shugaban kasa tare da hukumomin tsaro dukkansu na shirin shawo kan daukacin matsalolin tsaron a suka addabi Najeriya.

Boko Haram 

Najeriya ta dade tana fafutukar kawo karshen rikicin Boko Haram a arewa maso gabas wanda aka kwashe sama da shekaru 10 ana fafatawa, yayin da yayi sanadiyar kashe mutane sama da 36,000 da kuma raba sama da miliyan biyu da gidajen su abinda ya sa wasu daga cikin su samun mafaka a kasashen Chadi da Nijar da kuma Kamaru.

Buhari ya zo mulki da farin jina

Buhari ya zo karagar mulki da farin jini sosai a matsayin sa na tsohon shugaban kasa kuma kwamandan hafsan sojojin kasar abinda ya sa shi ya bayyana murkushe mayakan Boko Haram bayan karbar ragamar mulki a shekarar 2015, amma ko a wa’adin mulkin sa na farko Yan adawa na gabatar da korafi akan irin matakan da yake dauka akan matsalolin tsaro.

Shugabannin hafsoshin tsaron Najeriya a fadar gawamnatin kasar dake Abuja  yayin ganawar gaggawa kan tsaro ranar 30 ga watan Afrelun 2021 da shugaban kasa Muhammadu Buhari.
Shugabannin hafsoshin tsaron Najeriya a fadar gawamnatin kasar dake Abuja yayin ganawar gaggawa kan tsaro ranar 30 ga watan Afrelun 2021 da shugaban kasa Muhammadu Buhari. © Presidency of Nigeria

Dr Uche Igwe, mai bincike a Cibiyar tsaro ta LES Firoz Lalji dake Afirka yace sakamakon matsin lamba harma daga cikin abokan tafiyar sa, shugaban ya sauya shugabannin rundinonin tsaron kasa a farkon shekarar nan, kuma tun hawan sa karaga ake korafi kann matsalolin tsaron da kasar ke fuskanta.

Igwe yace magoya bayan sa da 'Yan adawa na bayyana damuwa kann gazawar sa da kuma yadda matsalolin suka dada karuwa.

A shekaru 6 da ya yi a karagar mulki, matsalolin tsaro sun dada ta’azzara a Najeriya kamar yadda masana suka bayyana, yayin da aka kasa shawo kan abinda ke haifar da su.

ISWAP

A arewa maso gabas, an samu nasarar korar mayakan Boko Haram daga yankunan da suke rike da su kafin fara mulkin Buhari, amma wani bangare na kungiyar da ya balle da ake kira ISWAP ta kara girma yadda ta dinga yin illa ga jami’an tsaro.

'Yan bindiga

A arewa maso yamma, hare haren da 'Yan bindiga suka kaddamar sun haifar da sace dimbin dalibai tun watan Disambar bara, abinda ya tada hankalin jama’a.

Rikici tsakanin al’ummomi ya dada karuwa tsakanin Fulani makiyaya daga arewacin Najeriya da kuma manoman dake kudancin kasar saboda mallakar filaye da abincin dabbobi da kuma ruwan sha, abinda ke haifar da fadace fadace.

Wani mai nazari kan harkokin tsaro a Faransa, Marc-Antoine Perouse de Montclas yace shugaba Buhari, kamar wadanda ya gada, baya bukatar kawo karshen wannan matsala ta sake fasalin rundonin tsaron kasa da Yan Sanda da yaki da cin hanci da kuma take hakkin Bil Adama.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.