Isa ga babban shafi
Najeriya - Buhari

Sace daliban Jangebe zai zama shi ne na karshe a Najeriya – Buhari

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya tabbatarwa ’yan Najeriya cewa daga satar daliban Makarantar Sakandiren Gwamnati ta ’Yan Mata dake Jangebe  a jihar Zamfara ba za a sake sace dalibai a makarantu ba.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari.
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari. © Nigeria Presidency
Talla

Sanarwar na Shugaban Buhari na kunshe ne cikin sakonsa da Ministan Sufurin Jiragen Saman Najeriya, Hadi Sirika ya isar yayin da ya jagoranci wata tawagar Gwamnatin Tarayya domin jajantawa Gwamnati da al’ummar jihar Zamfara kan iftila’in sace ‘yan matan.

Ministan ya ce, shugaban kasa ya ba da tabbacin ne, saboda gwamnatin ta bijiro da wasu sabbin matakai da zai kawo karshen ayyukan assha a fadin kasar.

“Shugaban Kasa ya damu matuka da sace wadannan daliban na Jangebe, kuma yana ba da tabbacin cewa gwamnati na da duk abubuwan da suka kamata wajen ganin an kawo karshen miyagun,”

inji shi.

Shugaba Buhari ya kuma jinjinawa Gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle kan irin kokarin da yake yi wajen yaki da ’yan bindiga, inda ya yi alkawarin ci gaba da bashi goyon bayan da ya dace don ganin an samu zaman lafiya mai daurewa a jihar.

Anashi jawabi, Gwamna Matawalle ya mika godiyar sa ga Buhari da Gwamnatin Tarayya, inda yace, nan bada jimawa ba za a ceto daliban na Jangebe.

Sauran wakilan dake cikin tawagar ta Gwamnatin Tarayyar sun hada da Ministan Harkokin ’Yan Sanda, Alhaji Maigari Dingyadi da Ministar Jinkai, Hajiya Sadiya Umar-Farouk da kuma Ministar Harkokin Mata, Misis Pauline Tallen.

A daren Jumma’ar da ta gabata, ‘yan bindiga suka kutsa Makarantar Sakandiren ’Yan Mata dake Jangebe a Karamar Hukumar Talata-Mafara, tare da sace sama da dalibai 300.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.