Isa ga babban shafi
Najeriya - Zamfara

Gudun hasarar rayukan fararen hula yasa bamu afkawa 'yan bindiga ba - Buhari

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya yi Allah wadai ta asarar da ‘yan bindiga ke yi a kasar, wanda a baya-bayan nan suka sace dalibai mata sama da 300 a wata makarantar sakandaren kwana dake Jangebe na Jahar Zamfara, yana mai cewa, ba zai“ ba da kai bori ya hau ba kan barazanar  ‘yan bindiga” da ke jiran “biyan kudin fansa ba.

Shugaban Najeriya Mohammadu Buhari yayin kaddamar da sabon shirin dakile rashin tsaron kafar intanet
Shugaban Najeriya Mohammadu Buhari yayin kaddamar da sabon shirin dakile rashin tsaron kafar intanet © Presidency of Nigeria
Talla

Rahotanni sun ce, da misalin karfe daya na daren Juma’a, ne “ ‘yan bindigar kan da suka iso garin kan Babura suka mamaye makarantar, kafin suyi awon gaba adadin matan da wasu majiya ke cewa sun zarta 600, ko da yake gwamnatin jihar ta tabbatar da adadin dalibai  317.

A cikin wata sanarwa da fadar gwamnatin Najeriya ta fitar a yammacin Jumma’a, shugaba Buhari ya bayyana cewa: "Wannan gwamnatin ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen murkushe 'yan fashi da ke addabar daliban da ba su ji ba basu gani ba, kawai don suna bukatan makudan kudaden fansa,"

Shugaban Ya kara da cewa:

 "Muna da karfin da za mu tura dakarunmu su mamaye dazukan da kuma murkushe 'yan ta'addan, to amma muna taka tsan-tsan saboda rayukan mazauna kauyukan da kuma wadanda aka yi garkuwar da su wadanda' yan ta'addar za su iya sadaukar da su.

A arewa maso yammacin Najeriya, matsalar tsaro na kara shiga wani mawuyacin hali kuma an bar mutane suna cin karensu ba babbaka don tabbatar da tsaron lafiyarsu.

A ranar Juma’a, wasu fusatattun mutane sun far wa ayarin motocin wani kwamishina da wani jami’in tsaro a kan hanyarsu ta zuwa Jangebe bayan sace daliban.

Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya, Antonio Guterres ya yi kira da a gaggauta sakin ‘yan matan sama da 300 da‘ yan bindiga suka sace a yankin arewa maso yammacin Najeriya, kamar yadda kakakinsa ya sanar ranar Juma’a.

Sakatare janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya bukaci sakin dalibai mata da aka sace a Najeriya

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.