Isa ga babban shafi
Zamfara-Dalibai

Iyayen daliban Zamfara sun yi kukan-kura sun shiga daji

Iyayen daliban Sankadaren Jangebe da ke jihar Zamfara sun yi kukan-kura, inda suka kutsa cikin daji domin tunkarar 'yan bindigar da suka sace 'ya'yansu a sanyin safiyar wannan Jumma'ar, yayin da gwamnati ta  bada umarnin rufe daukacin makarantun kwana da ke fadin jihar.

Zamfara na cikin tashin hankalin hare-haren 'yan bindiga
Zamfara na cikin tashin hankalin hare-haren 'yan bindiga © Channels
Talla

Sashen Hausa na RFI ya tattauna da mazauna yankin da lamarin ya faru kuma daya daga cikinsu da ya bukaci mu sakaya sunansa ya shaida mana cewa, iyayen daliban sun shiga cikin tawagar 'yan tauri da 'yan banga da  jami'an tsaro domin bibiyar sahun 'yan bindigar.

Mai magana da yawun gwamnatin jihar, Jailani Baffa ya tabbatar wa RFI Hausa cewa, tawagar jami'an tsaro da ta kunshi sojoji da 'yan sanda ta  fantsama cikin daji domin kwato daliban mata.

Tuni gwamnan jihar Bello Muhammad Matawalle ya bada umarnin rufe daukacin makarantun kwana da ke fadin jihar biyo bayan sace daruruwan daliban mata.

Rahotanni na ceawa, kimanin mata 600 aka yi awon gaba da su daga makarantar wadda ke Karamar Hukumar Talata Mafara kamar yadda daya daga cikin malaman makarantar ya shaida wa jaridar Daily Trust.

Gwamna Mutawalle ya shaida wa al’ummar jihar a wani jawabi ta kafar talabijin cewa, zuciyarsa na tare da iyalan daliban da lamarin ya shafa .

Gwamnan ya ce,

'Yan uwana mutanen Zamfara, wannan ba lokaci ne na dora wa juna laifi. Sabon salon hare-haren ‘yan bindiga ya bada damar daukar matakin  soji a daukacin jihohin da ke fama da matsalar.

Sai dai wasu daga cikin Zamfarawar da muka tattauna da su sun dora laifin sace daliban kan gwamnatin jihar saboda sulhun da ta ce, tana yi da 'yan bindigar tare da yi musu sassauci da kuma amsa bukatunsu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.