Isa ga babban shafi
Najeriya-Zamfara-Tsaro

Zamfara: Tsaro ya tabarbare a garin Shinkafi

Rahotanni daga Najeriya sun ce Yan bindiga a Jihar Zamfara sun mamaye kauyuka da dama a karamar hukumar Shinkafi, inda suka tare tawagar motocin sufuri, suka kashe mutane da kuma kora wasu cikin daji.

'Yan bindiga sun addabi jihar Zamfara ta Najeriya
'Yan bindiga sun addabi jihar Zamfara ta Najeriya © dailypost
Talla

Bayanai daga yankin sun ce yanzu haka wadannan Yan bindigar na iko da wasu kauyuka da dama.

Wannan ta’asa da ‘yan bindiga ke aikatawa na faruwa ne duk da matakan da hukumomin kasar suka dauka don sama wa al’umma sauki.

Majiyoyi daga yankin sun ce ko a makon da ya gabata, wadannan barayin daji sun ci karensu ba babaka, inda suka kwashe kwanaki 6 a jere suna da kisa da dibar mutane.

Kan haka ne Michael Kuduson ya tuntubi wani dan asalin garin Shinkafi, Hamdai Alhazzai Shinkafi, kuma ga tattaunawarsu

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.