Isa ga babban shafi
Najeriya - 'Yan bindiga

An rufe layukan Sadarwa a Zamfara saboda tsaro

A wani mataki na taimakawa jami’an tsaro gudanar da ayyukan dikile hare-haren ‘yan bindiga a jihar Zamfara gwamnatin Najeriya ta umurci daukacin kamfanonin sadarwar kasar da su katse layukan wayoyin salula a jihar.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari da hafsoshin tsron kasar yayin wani taron kan tsaro a fadarsa
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari da hafsoshin tsron kasar yayin wani taron kan tsaro a fadarsa © femi adeshina
Talla

Wata wasika mai dauke da sanya hannun shugaban Hukumar Sadarwa ta Kasa (NCC) da akayi ta yadawa ta bukaci katse hanyoyin sadarwar daga daukacin kamfanonin wayoyin Najeriya dake aiki a Jihar Zamfara.

Rahotanni sun ce umarnin rufe layukan sadarwar ya fara aiki ne tun ranar Juma’a  domin baiwa jami’an tsaro damar gudanar da ayyukan kakkabe ’yan bindiga dake samun bayanai kan duk wani mataki da ake dauka akansu.

Sai dai Hukumar Sadarwa ta kasa da kamfanonin sadarwar sun ki cewa komai akan wasikar da kuma umarnin.

'Yan bindiga

Umarnin rufe layukan sadarwa a Jihar Zamfara na zuwa ne kwana biyu bayan da ’yan bindiga suka kai hari a wata makarantar sakandare da ke kauyen Kaya a Karamar Hukumar Maradun ta jihar, inda suka yi awon gaba da dalibai maza da mata sama da 70.

Harin makarantar ya sa Gwamnatin Jihar Zamfara rufe makarantu a fadin jihar har sai abin da hali ya yi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.