Isa ga babban shafi
Najeriya - 'Yan bindiga

'Yan bindiga sun sako daliban kwalejin noma da suka sace a jihar Zamfara

Dalibai biyu cikin 15 da 'Yan bindiga sukayi garkuwa da su a kwalejin koyon aikin noma ta jihar Zamfara sun rasu yayin da kuma mahukunta a jihar suka bayyana nasarar kubutar da sauran da suka rage.

'Yan bindiga sun yi awon gaba da akalla mutane 40 a Shinkafi da ke jihar Zamfara a Najeriya
'Yan bindiga sun yi awon gaba da akalla mutane 40 a Shinkafi da ke jihar Zamfara a Najeriya RFI
Talla

Adadin mutane 20 ne dai aka yi garkuwa da su a harabar makarantar a ranar 16 ga wannan watar da muke ciki na Agusta bayan kashe mutane 3 nan ta ke a lokacin harin.

Yanzu dai jumlar mutane 18 hadi da dalibai da ma'aikata na kwalejin ne suka dawo gida, kamar yada SP Mohammed Shehu kakakin rundunar 'Yan Sandar jihar Zamfara ya yi wa sashin hausa na RFI karin bayani.

Kuna iya latsa alamar sauti domin saurarron abin da SP Mohammed Shehu ke cewa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.