Isa ga babban shafi
Najeriya-Zamfara

Jami'an tsaro sun ceto sama da mutane 500 daga 'yan bindiga a Zamfara

A Najeriya jami’an tsaro sun ceto mutane 544 daga hannu masu garkuwa da mutane a jihar Zamfara a cikin watanni biyu, kamar yadda gwamnan jihar Bello Matawalle ya bayyana a jiya Juma’a a  Gusau, babban birnin jihar.

Wani hoton abin misalin dake nuan 'yan bindiga.
Wani hoton abin misalin dake nuan 'yan bindiga. © PHOTO/FOTOSEARCH
Talla

Matawalle ya ce cikin wadanda aka ceto akwai mata da yara da tsofaffi, sai kuma wasu dalibai 2 na kwalejin gwamnatin tarayyar kasar ta birnin Yauri da aka sace a jihar Kebbi, da kuma dalibai 18 na kwalejin aikin noma ta Bakura, da kuma dalibai 75 na makarantar sakandaren Kaya dake karamar hukumar Maradun.

Gwamnan ya ce katse hanyoyin sadarwar da hukumomi suka yi a jihar ya taimaka wa jami’an tsaro wajen samun nasarori masu dimbim yawa a kokarin  samar da tsaro da yaki da ‘yan bindiga, ciki har da ceto wadanda aka yi garkuwa da su.

Ya ce jami’an tsaro sun yi nasarar kamo mutane da dama da ake zargi da aikata ayyukan ta’addanci da ma masu taimaka musu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.