Isa ga babban shafi
Najeriya-'Yan bindiga

'Yan bindigar Zamfara na neman tudun-mun-tsira

Rahotanni daga Najeriya na cewa, ‘yan bindigar jihar Zamfara na ci gaba da tserewa zuwa jihohi makwabta domin neman tudun-mun-tsira saboda yadda sojojin kasar ke ragargazar su babu kakkautawa.

'Yan bindiga sun addabi jihar Zamfara ta Najeriya
'Yan bindiga sun addabi jihar Zamfara ta Najeriya © dailypost
Talla

Jama’ar yankin sun rawaito cewa, ‘yan bindigar sun shiga cikin dimuwa duk da dai suna fasa shaguna domin sace abincin da za su ci gaba da ci a tudun-mun-tsirarsu.

Kazalika ‘yan bindigar sun sace wasu motoci  da kuma man fetur domin dura wa a cikin baburansu a yayin kokarinsu na ficewa daga jihar Zamfara.

Tuni dai wasu  jihohin makwabta kamar Sokoto suka fara daukar matakin dakile kwararowar ‘yan bindigar a cewar rahotonni.

‘Yan Najeriya da dama sun yaba wa gwamnatin tarayya kan wannan mataki da ta dauka na yi wa ‘yan bindigar luguden wuta bayan katse layukan sadarwa a jihar Zamfara domin gudanar da aikinsu ba tare da wata makarkashiya ba.

Sai dai wasu masharhanta kan lamurran tsaro na ganin cewa, ya kamata gwamnatin tarayyar ta dauki irin wannan mataki lokacin guda kan jihohin Kaduna da Katsina da Kebbi da Niger har ma da Zamfarar domin yi wa ‘yan bindigar kwab-daya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.