Isa ga babban shafi
Najeriya-'Yan bindiga

'Yan bindiga sun kashe mutane 33 a wani kauyen Zamfara

‘Yan bindiga a Jihar Zamfara da ke Najeriya, sun hallaka mutane 33 a Nasarawar Mai Fara ta karamar hukumar Tsafe da 'Yar Katsina da ke karamar hukumar Bungudu da kuma Nasarawa a karamar hukumar Bakura saboda abin da aka bayyana a matsayin gaza biyan harajin Naira miliyan 40 da barayin suka dora musu.

'Yan bindiga sun addabi jihar Zamfara ta Najeriya
'Yan bindiga sun addabi jihar Zamfara ta Najeriya © dailypost
Talla

Jaridar Premium Times da ake wallafawa a Najeriya ta ruwaito majiyoyi daga Nasarawar Mai Fara dake cewa an kai musu harin ne saboda gazawar da suka yi wajen biyan harajin miliyan 40 da 'yan bindigar suka sanya musu.

Majiyar ta ce kungiyar Ade Aleru, daya daga cikin manyan 'yan bindiga da suka addabi jihar, ta sanya musu harajin, wanda suka gaza biya.

Wani mazaunin Tsafe, Abubakar Balarabe dake aiki da Gidan Rediyo Thunder Blowers ya ce ya zuwa yammacin jiya, an tabbatar da mutuwar mutane 20.

A yankin Bakura kuma, wani jami’in kula da lafiya, Masud Kyambarawa ya ce an kashe mutane 3, cikin su har da limamin garin, Akilu Dan Malam.

Kyambarawa ya ce lokacin da aka fara harbe harbe, suna garin, inda suka je sa ido, abin da ya sa suka tsere zuwa kauyen Rabah dake Jihar Sokoto.

Jami’in ya bayyana halin da ake ciki a yankin a matsayin abin takaici, lura da yadda mata da yara ke gudu cikin daji domin tsira da rayukan su.

Jaridar ta ce 'yan bindigar sun hana mutane kauyen 'Yar Katsina zuwa Sallar juma’a, inda suka tarwatsa su a Masallaci lokacin da suka isa garin, abin da yayi sanadiyar kashe mutane 10.

Kakakin rundunar 'yan sandan Jihar Sokoto Mohammed Shehu, ya ce zai bincika kafin tabbatar da aukuwar lamarin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.