Isa ga babban shafi
Najeriya - Zamfara

Zamfara ta dora alhakin ta'addancin 'yan bindiga kan masu basu bayanai

Gwamnatin Zamfara ta zargi miyagun mutanen da suke baiwa ‘yan bindiga bayanai da hannu cikin munanan hare-haren da ‘yan ta’addan suka kai kan akalla kauyuka 10 a kananan hukumomin Anka da Bukuyyum.

Gwamnan jihar Zamfara Bello-Matawalle
Gwamnan jihar Zamfara Bello-Matawalle © Premiumtimes
Talla

Yayin tsokaci kan tashin hankalin, kwamishinan yada labaran gwamnatin jihar ta Zamfara, Ibrahim Dosara ne ya nanata zargin da ake yiwa miyagun mutanen da suka baiwa ‘yan bindiga bayanai, inda ya ce tuni dakarun soji suka fara farautar ‘yan ta’addan suka yiwa mummunar ta’asar a tsakiyar makon jiya.

Yanzu haka dai wasu majiyoyi a yankunan na Zamfara da suka fuskanci tashin hankalin sun ce adadin gawarwakin mutanen da ‘yan bindigar da ake kyautata zaton mabiya Bello Turji ne suka kashe, ya karu zuwa akalla 200, ko da yake gwamnati ba ta tabbatar da hakan a hukumance ba.

Sai dai yayin zantawa da sashin Hausa na RFI, Sarkin Dankon Bukuyyum Alhaji Muhammadu Usman ya ce adadin gawarwakin mutanen da suka gano tare da yi musu jana’iza 36 ne sabanin fiye da 100 a yankinsa.

00:58

Muryar Sarkin Dankon Bukuyyum Alhaji Muhammadu Usman

A karamar hukumar Anka kuwa mutane 22 masarautar yankin ta tabbatar da mutuwarsu a hare-haren 'yan bindigar.

A cikin makon da ya kare yayin wata zantawa da kafar talabijin ta Channels da aka watsa a ranar Laraba, shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya sha alwashin murkushe ‘yan bindigar da suka addabi yankin arewa maso yammacin kasar, wadanda ya bayyana a matsayin ‘yan ta’adda.

Yayin da ya ke amsa tambayoyi akan matsalar tsaro shugaba Buhari ya bayyana cewa ya tattauna da hukumomin tsaro akan ‘yan bindigar da gwamnatinsa ta ayyana a matsayin ‘yan ta’adda kuma za su dauki matakan da suka dace wajen murkushe ta’addancin nasu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.