Isa ga babban shafi
Najeriya

Buhari ya yi Allah wadai da ta'addancin 'yan bindiga a Zamfara

Shugaban Najeriya Muhd Buhari ya yi Allah wadai da kashe-kashen da ‘yan bindiga suka yi a jihar Zamfara cikin makon da ya kare.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari.
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari. AFP - LUDOVIC MARIN
Talla

Cikin sanarwar da ya fitar a ranar Asabar, shugaban Najeriyar ya bayyana kisan gillar da ‘yan ta’addan suka kai a wasu kauyukan kananan hukumomin Bukuyyum da Anka a matsayin huce fushinsu kan wadanda basu ji ba basu gani ba, sakamakon  farmakin da sojoji suka matsa wajen kai musu ta sama da kasa, wanda ya sha alwashin jami’an tsaron za su cigaba da aiwatarwa har sai sun murkushe miyagun.

A baya bayan nan ne dai, wasu majiyoyin gwamnati suka ce akalla mutane 58 suka mutu a hare-haren da ‘yan bindigar suka kai a tsakanin ranakun Laraba zuwa Alhamis, inda suka shafe kimanin sa’o’i 48 suna cin karensu babu babbaka.

Sai dai wasu alkaluman na daban, sun bayyana cewar yawan wadanda ‘yan ta’addan suka halaka ya kai kusan 200.

A cikin makon da ya kare yayin wata zantawa da kafar talabijin ta Channels da aka watsa a ranar Laraba, shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya sha alwashin murkushe ‘yan bindigar da suka addabi yankin arewa maso yammacin kasar, wadanda ya bayyana a matsayin ‘yan ta’adda.

Yayin da ya ke amsa tambayoyi akan matsalar tsaro shugaba Buhari ya bayyana cewa ya tattauna da hukumomin tsaro akan ‘yan bindigar da gwamnatinsa ta ayyana a matsayin ‘yan ta’adda kuma za su dauki matakan da suka dace wajen murkushe ta’addancin nasu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.