Isa ga babban shafi
Najeriya

Mutane 36 aka yi wa jana'iza ba fiye da 100 ba - Sarkin Bukuyyum

Sabbin bayanai daga karamar hukumar Bukuyyum da ke jihar Zamfara a arewa maso yammacin Najeriya, sun ce adadin mutanen da ‘yan ta’adda suka kashe, yayin hare-haren da suka kai a ranakun Laraba zuwa Alhamis, bai kai 100 ko sama da haka ba, kamar yadda kafafen yada labarai da dama suka ruwaito.

Hare-hren 'yan bindiga sun salwantar da rayuka da dama a arewacin Najeriya
Hare-hren 'yan bindiga sun salwantar da rayuka da dama a arewacin Najeriya Jakarta Globe
Talla

Sarkin Dankon Bukuyyum Alhaji Muhammadu Usman ne ya bayyana haka, a yayin wata zantawa ta wayar tarho da sashin Hausa na RFI, inda ya ce adadin gawarwakin mutanen da suka gano tare da yi musu jana’iza 36 ne sabanin fiye da 100.

00:58

Muryar Sarkin Dankon Bukuyyum Alhaji Muhammadu Usman

Ana dai kyautata zaton cewa, daruruwan ‘yan ta’addan da suka kaddamar da munanan hare-haren, masu biyayya ne da kasurgumin dan fashin dajin nan Bello Turji, wadanda hare-haren jiragen yakin sojin Najeriya ya tilastawa tserewa daga sansanoninsu da ke dajin Fakai a karamar hukumar Shinkafi.

Wani mazaunin yankin da ya shaida aukuwar lamarin, ya shaidawa jaridar Daily Trust da ke Najeriya cewar, ‘yan ta’addan sun rika budewa mutane ciki har da mata da kananan yara wuta da miyagun bindigogi da zarar sun yi yunkurin tserewa daga gidajensu da maharan suka cinnawa wuta.

Zalika adadin kauyukan da ‘yan bindigar suka afkawa ya kai akalla 10, sabanin 6 da akasarin kafofin yada labarai suka ruwaito.

Har zuwa lokacin wallafa wannan labari dai, babu cikakken bayan kan adadin mutanen da wannan tashin hankali ya rutsa da su a hukumance daga gwamnatin Jihar Zamfara ba da kuma hukumar ‘yan sanda.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.