Isa ga babban shafi
Najeriya-'Yan bindiga

'Yan bindiga sun kashe mutane 9 a Zamfara

Akalla mutane 9 ne suka mutu, kuma da dama suka rasa muhallansu a ranar Lahadi bayan da ‘yan bindiga suka kai wani hari cikin dare a kan wasu kauyuka  na karamar hukumar Tsafe ta jiha Zamfara.

Hoton 'yan bindiga somin misali.
Hoton 'yan bindiga somin misali. © India TV News / PTI
Talla

Kauyuka daga kananan hukumomin Tsafe ta jihar Zamfara da Faskari ta jihar Katsina na fama d hare hare na ‘yaan bindiga da ke cin karensu ba babbaka a karkashin kasurgumin dan ta’adda, Adamu Aleru da ya yi sansani a dajin Tsafe.

Wata majiya daga garin Tsafe ta sahida wa manema labarai cewa kauyukan da aka kai wa hare hare a daren Lahadi sun hada da Magazawa, Kajera, Unguwar Dan Halima, Unguwar Rogo, Unguwar Ango, Kurar Mota da Kauyen Kane dukkanninsu a karkashin gundumar Bilbis.

Majiyar ta ce ‘yan bindigar sun kaddamar da hare haren bai daya ne, amma mafi muni daga cikinsu shine na kauyen Magazawa, inda suka kashe mutane 7.

Ta ce babu labarin wadanda suka mutu a sauran kauyukan, amma mutanen kauyukan da dama sun arce daga gidajensu, tana mai cewa ta hango mata sama da 50 suna shigowa garin Tsafe da safiyar nan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.