Isa ga babban shafi

Luguden wutar Sojin saman Najeriya ya kashe 'yan bindiga 45 a Zamfara da Katsina

Wani lugeden wutar sojin saman Najeriya ya kashe ‘yan bindiga 45 ciki har da jagoransu Dogo Rabe yayin wani sumame da dakarun suka kai maboyar ‘yan ta’addan a dazukan jihohin Zamfara da Katsina na arewacin kasar.

Jiragen yakin Sojin saman Najeriya.
Jiragen yakin Sojin saman Najeriya. AFP PHOTO / STEPHANE YAS
Talla

Luguden Sojin saman Najeriyar a dazukan Zurmi da Birnin Magaji da kuma Jibia wanda ya kai ga mutuwar Dogo Rabe na zuwa kasa da kwanaki 4 bayan makamancinsa da dakarun suka kai maboyar Bello Turji da ya kai ga kisan ‘yan bindiga 22 ko da ya ke bayanai sun ce Turji ya tsere.

Yayin zantawar wani dan jaridar yankin Abdulbaqi Aliyu da jaridar kasar Premium Times ya yi ikirarin cewa harin sojin ya kashe ‘yan bindiga akalla 40 a yankin Birnin Magaji na jihar Zamfara.

Rundunar Sojin saman Najeriya ta ce hare-haren dakarunta a dajin sabon birnin dan Ali cikin karamar hukumar Birnin Magaji ya kashe ‘yan ta’adda 40, batagarin da wata majiya ke cewa suke aikata satar shanu a yankin.

Can a yankin Zurmi ma wani mazaunin garin Abdullahi Mamman ya ce harin Sojin ya kashe wani jagoran ‘yan bindigar Gwaska Dankarami.

A cewar Abdullahi Mamman babu tabbacin adadin ‘yan bindigar da aka kashe yayin farmakin domin kuwa adadi mai yaw ana batagarin na gudanar da wani taro ne a gidan jagoran nasu Dankarami lokacin da Sojin Najeriya suka jefa bom a cikin gidan.

Shaidar ya bayyana cewa har yanzu babu tabbacin ko jagoran na cikin wadanda aka kashe ko akasin haka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.