Isa ga babban shafi

Ruwa ya ci wasu mutane 5 a yayin da suke kokarin tsere wa 'yan bindiga a Abuja

Wasu mutane biyar da suka hada da maza hudu manya da matar aure daya sun nutse a ruwa, a lokacin da suke kokarin tserewa ‘yan bindigar da ke kokarin yin garkuwa da su, a kauyen Chakumi da ke unguwar Gurdi a karamar hukumar Abaji a birnin Abuja.

Hoton 'yan bindiga somin misali.
Hoton 'yan bindiga somin misali. © India TV News / PTI
Talla

Bayanai sun ce mutanen da suka rasa rayukansu, suna tsaka da aiki a gona a lokacin da ‘yan bindiga suka yi kokarin kama su, da misalin karfe 11 na safiyar ranar Laraba.

Yayin wata zantawa da jaridar Daily Trust  Najeriya, Sarkin Chakumi Muhd Magaji ya ce mutanen sun  garzaya domin  hawa kwalekwale su tsere zuwa kauyen Daku, amma a yayin da suke tsallaka kogin Gurara sai kwale-kwalen ya kife.

Basaraken ya koka da yadda ‘yaan bindiga suke cinkarensu babu babbaka ba tare da an kalubalance su baa, yana mai cewa yanzu al’ummarsa na tsoron zuwa gonakinsu.

Kakakin rundunar ‘yan sandan rundunar ‘yan sandan birnin tarayyar Abuja, adeh Josephine ba ta daga wayaa ba a lokacin da aka nemi karin bayani a game da lamarin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.