Isa ga babban shafi

Mutum 23 suka rage a hannun 'yan bindigar da suka sace fasinjojin jirgin kasa a Najeriya

Sama da fasinjoji 60 ne aka yi garkuwa da su a lokacin da ‘yan ta’adda suka far wa jirgin da ke jigilar su daga Abuja zuwa Kaduna, inda yanzu haka mutum 23 suka rage a hannun masu rike da makaman bayan kwanaki 186 da sace su.

Jirgin kasa da 'yan bindiga suka kai wa hari a watan Maris a kan hanyarsa daga Abuja zuwa Kaduna.
Jirgin kasa da 'yan bindiga suka kai wa hari a watan Maris a kan hanyarsa daga Abuja zuwa Kaduna. © Premium Times
Talla

Galibin fasinjojin da aka sako sun biya kudin fansa Naira miliyan 100 da ake zargin mawallafin da ke Kaduna, Tukur Mamu ya taimaka.

Hukumar DSS ta kama Mamu a makon jiya bisa zarginsa da alaka da ‘yan ta’adda.

Rahotanni sun nuna cewa tun lokacin da aka kama Mamu, sauran wadanda harin jirgin kasan ya rutsa da su ba su samu damar yin magana da danginsu ba.

Mohammed Sabiu Barau wanda kaninsa dan bautar kasa ke tsare a hannun ‘yan ta’addar har yanzu, ya shaidawa jaridar Daily Trust da ake wallafawa a kasar cewa, sun bar komai a hannun Allah.

A cewarsa, a matsayinsu na iyali, a kodayaushe suna fatan ganin ranar da za a sake shi ya koma gida.

"Muna cikin damuwa kowace rana amma a matsayinmu na Musulmai, muna da kyakkyawan fata game da makomarmu. Har yanzu muna addu'ar Allah ya sa mu dace. Kullum muna fatan ganin ya dawo gida amma har yanzu ba mu ji duriyarsa ba.

“Amma abin da muka ji kwanan nan shi ne kwamitin da gwamnati ta kafa don duba lamarin na yin wani abu a kai don haka muna fatan alheri,” inji Sabiu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.