Isa ga babban shafi

Jami'an tsaro sun dakile harin 'yan bindiga kan rumbun ajiyar hatsi a Katsina

Jami’an tsaron rundunar Civil Defence a jihar Katsina da ke arewacin Najeriya, sun dakile yunkurin da ‘yan bindiga suka yi na kai hari kan rumbun ajiyar kayayyakin abinci dangin hatsi na gwamnati, da ke yankin karamar hukumar Datsinma.

Wata bindiga mai daukar alburusai 50.
Wata bindiga mai daukar alburusai 50. AFP - STEFAN HEUNIS
Talla

Cikin sanarwar da ya fitar a yau Lahadi, kakakin rundunar tsaron ta Civil Defence Buhari Hamisu, ya ce ‘yan bindigar sun kai farmakin ne da misalin karfe 1 na daren ranar Asabar, da zummar fasa rumbun ajiyar abincin da kuma sace manajan da ke kula da rumbun mai suna Lawal Shitu ‘Yar’adua.

Kakakin ya ce sai dai dakarunsu suka shafe sama da sa’o’i biyu suna musayar wuta da maharan kafin daga bisani Allah ya basu sa’ar fatattakarsu bayan jikkata da dama daga cikinsu, kodayake sun tsere.

Bayanai sun ce mahukunta na amfani da  majiya ko  katafaren rumbun hatsin da ‘yan ta’addan suka kai wa farmaki ne wajen rarraba wa wasu daga cikin mazauna jihohin Katsina da Sokoto da kuma Zamfara tallafin abinci.

Harin na ranar Asabar ya zo ne kwana guda bayan da ‘Yan Sanda a jihar ta Katsina  suka sanar da kashe wasu ‘yan bindiga 5, tare da ceto mutane fiye da 100 da ‘yan ta’addan suka yi garkuwa da su, yayin da kuma suka kwato shanu  658 daga hannun barayin, nasarorin da rundunar ‘Yan Sandan ta ce ta samu daga 1 zuwa 31 ga watan Maris.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.