Isa ga babban shafi

'Yan bindiga sun bude wuta a kan ayarin 'yan kasuwa a Katsina

A Najeriya, ‘yan bindiga sun kashe wasu ‘yan kasuwa hudu a karamar hukumar Jibia ta jihar Katsina a jiya Lahadi.

Misali na 'yan bindiga.
Misali na 'yan bindiga. © Daily Trust
Talla

Rahotanni suka ce ’yan kasuwar da suka fito daga kauyen Zandam, na kan hanyarsu ta zuwa wata kasuwa da ke kusa da hedikwatar karamar hukumar ne a lokacin da suka ci karo da ‘yan bindigar.

Kakakin ‘yan sandan jihar Katsina SP Gambo Isah ya tabbata da aukuwar lamarin,  ya bayyanaa cewa ‘yan bindigar sun harbe ‘yan kasuwa 5, inda 4 suka mutu nan take.

Mazauna yankin sun ce lamarin ya haddasa tsoro da fargaba a tsakanin sauran ‘yan kasuwar da suka riga suka isa kasuwar tun da wuri.

Sai dai rahotanni sun ce hankula na kwance a cikin garin Jibiyar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.