Isa ga babban shafi

'Yan bindiga sun bukaci a biya Naira miliyan 30 kan ma'aikatan gona a Katsina

Kwanaki 3 bayan da ‘yan bindiga suka yi garkuwa da wasu ma’aikatan gona fiye da 40 a jihar katsina ciki har da kananan yara 39, masu garkuwar sun bukaci a biya su fansar miliyan 30 gabanin sakin mutanen.

'Yan bindiga a Najeriya
'Yan bindiga a Najeriya © dailypost
Talla

‘Yan bindigar sun bukaci tattaunawa don yin sulhu da mamallakin gonar da suka kwashe ma’aikatan a ciki, yayinda suka sha alwashin cewa wajibi a biya dukkanin kudin da suka bukata gabanin sakin mutanen.  

Tuni dai iyayen yaran 39 da ‘yan bindigar suka yi garkuwa da su suka fara aikewa da rokon su ga gwamnati don ganin an kubutar da yaran nasu wajen biyan kudin Naira miliyan 30 da masu garkuwar suka bukata.

A ranar lahadin da ta gabata ne, ‘yan bindigar suka afkawa masu aiki a wata gona da ke kauyen Mairuwa a karamar hukumar Faskari ta jihar Katsina tare da kwashe masu kwadago fiye da mutum 40.

Majiyar ta ce ‘yan bindigan sun ce mai gonar, wanda sai da ya biya Naira miliyan guda kafin suka ba shi damar girbe hatsinsa suka zo daukewa, amma suka yi awon gaba da yaran tun da ba ya nan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.