Isa ga babban shafi

Najeriya: 'Yan bindiga sun yi garkuwa da majinyata a jihar Neja

Akalla mutane biyu ne aka kashe yayin wani hari da ‘yan bindiga suka kaddamar a babban asibitin Abdulsalami Abubakar da ke Gulu a karamar hukumar Lapai ta jihar Neja a daren ranar Litinin.

Misali na 'yan bindiga.
Misali na 'yan bindiga. © Daily Trust
Talla

Kawo yanzu dai ba a tantance sunayen wadanda aka kashen ba, said ai an tabbatar da cewa daga cikin wadanda aka sace akwai Likita, ma’aikatan jinya da kuma marasa lafiya da ‘yan uwansu.

Rahotanni na cewa daga cikin ma’aikatan asibitin da aka sace akwai shugaban, sashen kula da matsalolin marasa lafiya, Dakta John, Shugaban bangaren kula da matsalolin jini, Usman Zabbo, da ma’aikacin dakin binciken lafiya, Awaisu Bida.

Haka kuma an sace matar shugaban ma’aikatan jinya da ‘ya’yansa mata, da kuma mata da diyar babban likitan ko kuma masani a bangaren magunguna, da sauran ‘yan uwan majinyata.

Wani ma’aikacin da ba ya bakin aiki a lokacin da aka kai harin ya shaida wa Daily Trust cewa an yi garkuwa da marasa lafiya.

Ya ce maharan da suka shafe sa’o’i da dama su na harbe-harbe ba tare da wata tangarda ba, yayin da ‘yan sa kai suka yi ta tserewa domin ceton rayukansu, majinyata sun shiga rudani sosai.

Mutane da dama musamman mata da yara sun gudu zuwa kauyukan da ke makwabtaka da garin Lapai, hedikwatar karamar hukumar.

Har yanzu ‘yan sanda ba su ce uffan ba. Sai dai jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Neja, DSP Wasiu Abiodun, ya yi alkawarin zai bayar da cikakken bayan ikan lamarin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.