Isa ga babban shafi

'Yan bindiga sun sace daliban Jami'ar Nsukka kwana kadan bayan janye yajin aikin ASUU

‘Yan bindiga sun yi awon gaba da daliban jami’ar Najeriya ta Nsukka a kudu maso gabashin kasar da ke kan hanyarsu ta komawa makaranta bayan janye yajen aikin tsawon watanni 8 da kungiyar malaman jami’o'in kasar ta ASUU ta yi.

Wani hoton misalin da ke nuna 'yan bindiga a Najeriya.
Wani hoton misalin da ke nuna 'yan bindiga a Najeriya. © PHOTO/FOTOSEARCH
Talla

Rahotanni sun ce lamarin ya afku ne da misalin karfe 4 na yamma agogon Najeriya a ranar Lahadin da ta gabata a kan hanyar Nsukka zuwa Opi da ke karamar hukumar Igbo-Etiti ta jihar Enugu a kudu maso gabashin Najeriya.

Baya  ga wadannan daliban jami’a da ba a fayyace adadinsu ba, ‘yan bindigar sun kwashe fasinjoji kamar yadda wasu majiyoyi suka bayyana, inda suka ce har a ranar talatar nan sai da suka ci gaba da aikata aika-aika a wannan hanyar.

Har ila yau wasu majiyoyi na dabam sun ce motoci 6 ne wadannan masu dauke da makamai suka tare, kana suka kwashe ilahirin wadanda ke cikinsu har da daliban jami’ar Najeriyar ta Nsukka.

Rundunar ‘yan sanda jihar wadda ta tabbatar da afkuwar wannan al’amari, ta ce ta na yin duk mai yiwuwa wajen ceto wadanda aka sacen, sai dai itama bata bayyana adadin yawan daliban da kuma sauran fasinjan da aka sace ba.

Kakakin ‘yan sandan jihar ta Enugu, Daniel Ndukwe, wanda ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar a Laraba inda ya ce jami'an na aikin laluben inda 'yan bindigar suka kai tarin mutane la'akari da cewa har zuwa yanzu basu tuntubi iyalan mutanen da ke hannunsa ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.