Isa ga babban shafi

An yankewa 'yan bindigar da suka kitsa harin ta'addanci a Afirka ta tsakiya hukunci

A wani hukunci mai cike da tarihi, wata kotu da ke samun goyon bayan majalisar dinkin duniya a Jamhuriyar Afrika ta tsakiya, ta yankewa wasu ‘yan bindiga uku hukunci gameda laifin cin zarafin bil adama da suka aikata. 

Misali na 'yan bindiga.
Misali na 'yan bindiga. © Daily Trust
Talla

Kotun dai ta yankewa Issa Sallet Adoum da Ousman Yaouba da kuma Tahir Mahamat hukuncin ne bayan samun su da hannu wajen kai wani harin ta’addancin da ya sanadiyar mutuwar mutane 46 a arewa maso yammacin kasar a watan Mayun shekarar 2019.

Kotun ta musamman da ke dauke da alkalai na ciki da wajen kasar ta yankewa Adoum hukuncin daurin rai da rai yayinda sauran mutane biyun aka yanke musu hukuncin shekaru 20 a gidan yari.

Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya wacce daya ce daga cikin kasashe mafi talauci da kuma tashin hankali a duniya, ta fada cikin yakin basasa ne a shekarar 2013 sanadiyar bangaranci.

An samu saukin tashe-tashen hankula a kasar ne a cikin shekarar 2018, amma sai dai a farkon shekarar 2021, kashi biyu bisa uku na kasar ya fada hannun kungiyoyin masu dauke da makamai.

A shekarar 2015 ne aka samar da kotun da ke samun goyon bayan MDD, sai dai tsawon shekaru ta sha fama da koma baya dalilin rashin kudi da sauran su.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.