Isa ga babban shafi

'Yan bindiga sun kashe mutane 3 tare da sace gommai a Kaduna da Katsina

Rahotanni daga jihar Kaduna sun tabbatar da yadda wani gungun ‘yan bindiga da suka farmaki garin Birnin Gwari da ke jihar Kaduna ta arewacin kasar suka kashe wani sufeton dan sanda tare da mutane 3.

'Yan bindiga sun addabi jihar Zamfara ta Najeriya
'Yan bindiga sun addabi jihar Zamfara ta Najeriya © dailypost
Talla

Shaidun gani da ido da ke tabbatarwa faruwar harin, sun ce da misalin karfe 7:30 na daren asabar din karshen makon jiya ne, ‘yan bindigar suka farmaki yankin Hayin Gada da ke garin Damari a mazabar Kazage tare da sace mutane 12 baya ga kashe wasu 3.

A cewar rahotannin cikin wadanda ‘yan bindigar suka kashe har da Sanusi Zubairu da kuma Kabiru Zubairu yayinda kuma suka fasa shagunan jama’a tare da sace tarin kayaki.

Tuni dai masarautar Birni-Gwari ta tabbatar da faruwar harin a yau talata, inda ta ce akwai kuma wani hari na daban da ya hallaka mutum guda yayinda ‘yan bindigar suka sace wasu mutum 6 akan babban titin yankin.

Haka zalika ‘yan bindigar sun kuma kashe wasu mutum 4 a titin Dajin jangali baya ga sace mashina masu kafa biyu kirar Bajaj guda 3 daga manoma a yankin kamfanin Doka.

A wani labarin na daban ‘yan bindigar sun kuma kashe sufeton ‘yan sanda Idris Musa tare da koma motarshi a kan hanyar Katsina zuwa Jibia yayinda kuma suka sace gomman fasinjoji akan hanyar Makera da ke tsakar jihar ta Katsina.

Shaidun gani da ido sun ce da sanyin safiya ne ‘yan bindigar suka tare babbar hanyar shiga Katsina tare da kora tarin fasinjojin haya cikin daji.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.