Isa ga babban shafi

'Yan bindiga sun nemi kudin fansa na Naira miliyan 250 a wajen wasu 'yan Katsina

Rahotanni daga jihar Katsina a Najeriya sun ce al’ummar kauyen Bakiyawa da ke yankin Batagarawa na cikin firgici bayan da ‘yan ta’addan da suka sace mazauna kauyen 43 suka bukaci da a biya su naira miliyan 250 a matsayin kudin fansa, kafin sako mutanen da suke yi garkuwa da su.

Misali na 'yan bindiga.
Misali na 'yan bindiga. © Daily Trust
Talla

Majiyoyi da dama sun ce, ‘yan ta’addan sun kaiwa kauyen na Bakiyawa farmaki ne a ranar Laraba, 14 ga watan nan na Satumba, inda suka kashe mazauna garin hudu, tare da yin garkuwa da wasu mutane 44, sai satar da suka yi daga shaguna da kuma kore shanu da dama.

Rahotani daga yankin na cewa ana cikin haalin rashin tabbas a game da makomar wadanda ‘yan bindigar ssuka dauke, duba da cewa babu alamun hada wadannan makudan kudade da ake nema  a matsayin fansa.

Kakakin runduna ‘yan sandan jihar, Gambo Isa ya ce babu wani bayani da ya samu a hukumnce a game da kudin fans ana naira miliyan 250 da ‘yan bindigar suke nema.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.