Isa ga babban shafi

‘Yan bindiga sun kashe jami’an ‘yan sandan kwantar da tarzoma 5 a Katsina

A Najeriya wasu ‘yan bindiga sun kashe jami’an ‘yan sandan kwantar da tarzoma 5 da wasu fararen hula 12 a  jerryin hare -haren da suka kai musaman a  shingen binciken ababen hawa a karamar hukumar Kankara ta jihar Katsina, a arewa maso yammacin kasar.

Wani kauye da 'yan bindiga suka tilastawa mutane masu yawan gaske tsrewa a karamar hukumar Jibiya dake jihar Katsina a Najeriya.
Wani kauye da 'yan bindiga suka tilastawa mutane masu yawan gaske tsrewa a karamar hukumar Jibiya dake jihar Katsina a Najeriya. © Daily Trust
Talla

Wata majiya ta ce ‘yan bindigan da suka kai kimanin 300, bisa babura, dauke da muggan makamai sun fito ne daga sansanin kasurgumin dan bindigan nan da aka nada wa sarautar sarkin Fulani a makon da ya gabata a jihar Zamfara, wato Ado Aleru.

Wani rahoto daga mazauna yankin na nuni cewa akalla mutane hudu ne suka mutu tsakanin talata da laraba biyo bayan wasu hare-hare a kauyen Faskari.

Kakakin ‘yan sandan jihar Katsina, Gambo Isah, wanda ya tabbatar da aukuwar lamarin, ya ce ‘yan bindigan sun yi wannan aika aika ne da misalin karfe 6 da rabi na yammacin Laraba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.