Gwamnan Katsina ya ba da umarnin maida layukan sadarwa a kananan hukumomi 10
Gwamnan Katsina Aminu Bello Masari ya bukaci hukumar sadarwar Najeriya NCC, da ta dawo da layukan sadarwa a kananan hukumomi goma daga cikin 17 da dokar katse layukan ta shafa, wadda aka kafa kimanin watanni hudu da suka gabata.
Wallafawa ranar:
Daraktan yada labaran Gwamnan na Abdu Labaran Malumfashi ya ce kananan hukumomin goma da aka maidawa layukan sadarwar sun hada da Matazu, Musawa, Kurfi, Dutsinma, Kafur, Malumfashi, Dandume, Bakori, Funtua, da kuma Danja.
Kananan hukumomin da dokar katse layukan sadarwar za ta ci gaba da aiki kuwa sun hada da Sabuwa, da Faskari, da Batsari, Safana, Kankara, da Danmusa da kuma Jibia.
Daraktan watsa labaran na Katsina ya ce gwamnati ta yanke shawarar daukar matakin ne sakamakon samun saukin da aka samu na hare-haren ‘yan bindigar da suka adabi jama’a a sassan yankunan.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu