An katse layukan sadarwa a wasu yankunan jihar Katsina
Bayanai daga jihar Katsina a tarayyar Najeriya sun ce an katse layukan wayoyin sadarwa a kananan hukumomi 13 da ke fama da hare-haren ‘yan bindiga.
Wallafawa ranar:
Kananan hukumomin da matakin ya shafa sun hada da Sabuwa, Faskari, Dandume, Batsari, Danmusa, Kankara, Jibia, Safana, Dutsin-Ma da Kurfi, sai kuma Funtua, Bakori da Malumfashi, wadanda ke kusa da dajin Ruggu inda mafi yawan 'yan bindigar ke buya.
A baya bayan nan ne dai Hukumar kula da Sadarwa ta Najeriya NCC ta musanta shirin rufe layukan sadarwa a jihar Katsina.
A farkon watan Satumban da muke hukumar ta NCC ta baiwa kamfanonin sadarwa umarnin rufe dukkanin layukansu a jihar Zamfara mai makwabtaka Katsina daga ranar 3 ga watan na Satumba, domin baiwa hukumomin tsaro damar gudanar da ayyukan kawo karshen ‘yan bindigar da suka addabi jama’a.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu