Isa ga babban shafi
Najeriya-Katsina-'Yan bindiga

'Yan bindiga sun kashe mutane 12 tare da yi wa mata fyade a Katsina

A Najeriya ‘yan bindiga sun kashe mutane 12 tare da raunata da dama a wani harin da suka kai kauyen Duba dake karamar hukumar Batsari ta jihar Katsina.

Hare haren 'yan bindiga na ci gaba da ci wa arewacin Najeriya tuwo a kwarya.
Hare haren 'yan bindiga na ci gaba da ci wa arewacin Najeriya tuwo a kwarya. © Social News XYZ
Talla

Wani mazaunin garin Batsari da ya nemi a sakaya sunansa ya ce ‘yan bindigar sun afka wa  kauyen wanda nisan kilomita kalilan ne tsaninsa da Batsari  da yamacin Asabar ne, inda suka yi wa dimbim mata fyade tareda yin awon gaba da dabbobi da dama.

Rahotanni sun ce ‘yan bindigar da suka wa kauyen sun ci Karensu ba babbaka ba tare da fuskantar turjiya ba. Kuma bayan mutane 12 da suka mutu, yanzu ana nan ana neman mutane da suka bace a dazukan kusa da kauyen.

Ya zuwa lokacin hada wannan labari, babu wata hukuma da ta tabbatar da aukuwar lamarin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.