Isa ga babban shafi
Najeriya-'Yan bindiga

'Yan bindiga sun sace daliban Islamiyya 9 a Katsina

Rahotanni daga arewacin Najeriya sun ce wasu ‘yan bindiga sun sace daliban makarantar Islamiyya 9 a wani kauye da ke jihar Katsina mai fama da matsalar garkuwa da mutane.

Gwamnan Jihar Katsina Aminu Bello Masari.
Gwamnan Jihar Katsina Aminu Bello Masari. © The Guardian Nigeria
Talla

Ganau sun tabbatar da yadda ‘yan bindigar suka shiga kauyen na Sakki haye a babura inda suka yi awon gaba da dalibai 8 da kuma malami guda lokacin da yaran ke kokarin komawa gida bayan tasowa daga Islamiyya.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Gambo Isah da ke tabbatar da faruwar lamarin ya ce  jami’ansu yanzu haka na aiki tukuru don ganin sun kubutar da yaran 9.

Wani mazaunin garin Muntari Nasiru ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa da misalin karfe 6 na yammaci ne ‘yan bindigar suka shiga garin na Sakki tare da shan gaban yaran da malaminsu guda lokacin da su ke kokarin komawa gida bayan tashi daga Islamiyya.

Nasiru ya ci gaba da cewa ‘yan bindigar sun yiwa yaran da malaminsu guda barazana tare da tilasta musu hawa kan baburan inda suka shige da su cikin daji.

Satar mutane don neman fansa musamman dalibai a jihar ta Katsina ba sabon abu ba ne inda ko a watan Disamban bara ‘yan bindigar suka sace wasu daliban Islamiyya fiye da 100 a kauyen Baure gabanin nasarar ceto su daga bisani.

 Wani rahoton Majalisar Dinkin Duniya ya nuna yadda ‘yan bindigar suka sace daliban da yawansu ya kai 950 daga watan Disamban bara zuwa yanzu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.