Isa ga babban shafi
Najeriya-'Yan bindiga

Sojin Najeriya sun kashe 'yan bindiga 78 a Zamfara

Rundunar sojin saman Najeriya ta sanar da kashe ‘yan bindiga alalla 78 a wasu hare-haren da ta kai a wasu dazuka da ke cikin jihar Zamfara arewa maso yammacin kasar.

Wani jirgin yakin Najeriya.
Wani jirgin yakin Najeriya. AP - Sunday Alamba
Talla

Kakakin rundunar sojin saman Edward Gabkwet ya bayyana a wata sanarwar da ya fitar a ranar Alhamis cewa, an kashe ‘yan bingida 78 tare da lalata sansanoninsu da dama a jerin hare-haren da aka kai masu ta sama.

Sanarwar ta ci gaba da cewa, an kai hare-haren ne a ranar 2 ga wannan wata na Agusta a gandun-dajin Kuyanbana da ke cikin jihar ta Zamfara inda ‘yan bindigar suka share tsawon shekaru suna addabar mazauna yankin.

A cikin watannin da suka gabata, rundunar sojin Najeriya ta sanar da tura karin sojoji da kuma kayan aiki zuwa yankin don murkushe ‘yan bindigar, wadanda da farko ke satar dabbobi, kafin daga bisani su fara yin garkuwa da mutane ciki har da dalibai domin neman kudin fansa.

A cewar wasu alkaluma da kungiyar International Crisis Group ta fitar cikin watan Mayun da ya gabata, adadin wadanda suka rasa rayukansu sanadiyyar hare-haren ‘yan bindiga cikin jihohin Niger, Katsina, Zamfara da kuma Kaduna sun zarta dubu 8.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.