Isa ga babban shafi

'Yan bindiga sun sace matan aure a gidajensu a Katsina

‘Yan bindiga sun sace matan aure guda hudu tare da kananan yara biyar bayan sun kai hari a rukunin gidaje na Shema Quarters da ke Karamar Hukumar Dutsin-Ma ta jihar Katsina da ke Najeriya.

'Yan bindiga na cin karensu babu babbaka a arewacin Najeriya.
'Yan bindiga na cin karensu babu babbaka a arewacin Najeriya. © dailypost
Talla

Rahotanni sun ce, mazajen wadannan matan sun tsere daga gidajensu bayan sun fahimci kokarin ‘yan bindigar na kutsawa cikin gidajensu.

Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa, ‘yan bindigar sun dirar wa gidajen ne da misalin karfe 11 da rabi na dare a jiya Lahadi kuma sun kwashe mintuna 30 suna cin karensu babu babbaka kafin isowar jami’an tsaro.

Daya daga cikin mazauna rukunin gidajen da ya bukaci a sakaya sunansa ya ce, a karon farko kenan da wadannan ‘yan bindigar ke kaddamar musu da hari.

Wannan na zuwa ne bayan ‘yan makwanni da ‘yan bindigar suka kashe Kwamandan ‘yan sandan Dutsinma, ACP Aminu Umar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.